Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Da ɗumi-ɗumi: Majalisar dokokin Kano ta Sahale kasafin baɗi

Published

on

Majalisar dokokin jihar Kano, ta sahale ƙudurin dokar kasafin kuɗin baɗi na fiye da Naira biliyan 437 i zuwa doka.

Ƙudurin kasafin, ya samu wannan nasara ne a zaman majalisar na yau Laraba ƙarƙashin jagorancin shugaban majalisar Alhaji Jibril Isma’il Falgore.

Da ya ke yin ƙarin haske kan sahale kasafin, shugaban masu rinjaye na majalisar Alhaji Lawan Hussaini Chediyar ƴan Gurasa, ya bayyana cewa, jimillar kasafin ya kai kimanin naira biliyan ɗari huɗu da talatin da bakwai da miliyan ɗari uku da talatin da takwas da dubu ɗari uku da sha biyu da naira ɗari bakwai da tamanin da bakwai da kwabo goma sha tara.

Haka kuma ya ƙara da cewa, ”Kimanin kaso sittin da shida na kasafin an ware su ne wajen gudanar da manyan ayyuka, yayin da aka ware kaso talatin da hudu wajen tafiyar da ayyukan gwamnati.”

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!