Labarai
Da ɗumi-ɗumi: An ɗage shari’ar Ɗansarauniya saboda ta Abduljabbar
Kotun majistiri mai lamba 58 ta ɗage zamanta na gobe Alhamis 3 ga watan Fabrairu a kan zargin da ƴansanda ke yiwa tsohon Kwamishinan Ayyuka Injiniya Mu’azu Magaji Ɗansarauniya saboda shari’ar Malam Abduljabbar Kabara.
Mai Shari’a Aminu Gabari ne ya ɗage zaman daga 3 ga wata zuwa 4 ga watan na Fabrairu sakamakon yanayin tsaro kuma a ranar 3 ga watan ne za a ci gaba da Shari’ar Abduljabbar Nasiru Kabara.
Kotun ta yi la’akari da cewar ana jibge jami’an tsaro a Shari’ar Abduljabbar haka zalika ita ma Shari’ar Ɗansarauniyar tana buƙatur a jibge jami’an tsaro.
Ana dai zargin Ɗansarauniyar da laifin cin mutuncin gwamnan Kano Dr Abdullahi Ganduje ta hanyar yaɗa wani hoto a shafinsa na Facebook.
Wakilin Freedom Radio Yusuf Nadabo Isma’il ya ruwaito cewar kotun za ta bayyana matsayarta kan roƙon da lauyan kariya ya yi na neman beli a ranar 4 ga wata maimakon 3 ga wata da aka sanya da farko.
You must be logged in to post a comment Login