Labarai
Da ɗumi-ɗumi: Kano Pillars ta lallasa Wikki Tourist

Ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Kano Pillars ta lallasa Wikki Tourist ta jihar Bauchi da ci ɗaya mai ban haushi.
Kano Pillars ta yi nasarar ne a wasan sada zumunta da aka gabatar da yammacin Asabar a filin wasa na Dutse Township da ke jihar Jigawa
Ɗan wasan Pillars Ali Rabi’u ne ya jefa ƙwallon yayin da ake tsaka da buga wasan.
A ranar Lahadi ma Kano Pillars ɗin zata buga wasan sada zumunta da ƙungiyar El-kanemi ta jihar Borno.
You must be logged in to post a comment Login