Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labaran Wasanni

Kano Pillars ta lallasa Gaida United da ci 5-0

Published

on

Kungiyar kwallon kafa ta Kano Pillars ta lallasa kungiyar Gaida United da ci 5-0 a wasan sada zamunci da suka fafata.

Karawar data gudana a filin wasa na Sani Abach da ke unguwar Kofar Mata a ranar Lahadi 03 ga watan Oktoban 2021 da muke ciki.

Dan wasan kungiyar ta Kano Pillars Nwachukwu ne ya zura kwallaye biyu a minti na 36 da kuma ’37’ da wasan.

Yayin da ‘yan wasa Alhaji Chilin da Kabiru Sunusi da kuma Musa Ahmad suka zura kwallaye dai-dai a minti na 63′ da 68′ da kuma 89’.

Kungiyar da akewa take da Sai Masu gida na cigaba da gudanar da wasannin sada zumunci domin tunkarar kakar wasannin shekarar 2021/2022.

Bayan da kungiyar ta kammala a mataki na biyar a kakar wasannin data gabata da maki 64 a wasanni 38 data buga.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!