Labarai
Da ɗumi-ɗumi: Kotu ta bayar da belin Bashir Ɗandandago
Kotun Majistiri mai lamba 58 da ke Noman’s Land a nan Kano, ta bayar da belin mawaƙin yabon nan Malam Bashir Ɗandago.
A yayin zaman kotun na ranar Talata, an karanto wa Bashir Ɗandago tuhumar da ake masa wanda kuma ya musanta.
A nan ne lauyan sa Barista Rabi’u Shu’aibu Abdullahi ya nemi da a bada belinsa.
Mai shari’a Aminu Gabari ya amince da buƙatar inda ya bayar da belin sa, bisa wasu sharuɗa.
Sharuɗan sun haɗa da ya kawo cikakkun mutane biyar, ɗaya daga ciki ya zama Kwamandan Hisbah na ƙaramar hukumar Gwale.
Ɗaya daga ciki kuma ya zama mai unguwar inda mawaƙin ya ke zaune, idan ba a samu ɗaya daga ciki ba sai ya musanya da wakilin sa.
Sannan kotun ta sanya za a ajiye kuɗi dubu ɗari biyar.
You must be logged in to post a comment Login