Connect with us

Tsaro

Da ɗumi-ɗumi: Za a dawo da zirga-zirgar jiragen ƙasa – NRC

Published

on

Hukumar kula da zirga-zirgar jiragen ƙasa ta ƙasar nan ta sanar da sake dawo da zirga-zirgar jiragen daga Abuja zuwa Kaduna.

Wannan na zuwa ne awanni 24 bayan wani hari da aka kai wa wani jirgin ƙasa a ranar Alhamis akan hanyar sa ta zuwa Kaduna daga Abuja.

Bayanin hakan na cikin wata sanarwa da hukumar ta fitar ranar Juma’a.

Cikin sanarwar hukumar na sanar da jama’a, musamman fasinjojin da ke bin hanyoyin cewa a za ci gaba da jigilar su gobe, ranar Asabar 23 ga Oktoban 2021.

Tuni dai hukumar ta bayyana rashin jin daɗin ta kan harin da aka kai wa jiragen ƙasa har sau biyu a jere.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!