Coronavirus
Da alama an kama hanyar Rayuwa bayan Corona a Jigawa
Rayuwa da corona wani darasi ne babba kuma mai zaman kansa lura da tarin kalubalen da al’umma suka shiga, sakamakon dokar zaman gida da kuma takaita zirga-zirga wadda hakan babbar kishiya ce ga duk wata hada-hadar kasuwanci da sufuri.
A jjhar Jigawa dai yanzu an shiga mako na biyu da bude ko ina da ina domin kuwa babu koda gari guda dake karkashin dokar kulle a jihar, wadda hakan ke da nasaba da samun saukin sabbin masu kamuwa da Corona a jihar baki daya.
Mutane sun shafe makonni ba tare da zuwa Kasuwa ko samun damar yawo ba, yayin da su ma ma’aikata gwamnatin jihar ta sanar da kara tsawaita musu dokar yin aiki daga gida.
Shin ko yaya rayuwa take a bangaren al’ummar gari bayan dage dokar lockdown.
Wasu al’ummar Jigawa da Freedom Radio ta zanta dasu sun ce har yanzu al’amuran basu dawo yadda yakamata ba kamar yadda aka saba kafin bullar cutar Corona.
Malam Nura Muhammad wani matashi ne kuma magidanci yace duk da har yanzu gari bai ware ba amma fa baza a kwatanta da baya ba, domin a baya ba a samun damar fitowa yanzu kuma akan fita a nemi na kalaci.
Al’ummar jihar ta Jigawa sun yi fatan samun dauki daga gurin mahukunta sakamakon halin da kana nan yan kasuwa suka shiga sanadiyyar zaman gida saboda Corona da akayi a baya.
You must be logged in to post a comment Login