Coronavirus
Da dumi-dumi: An janye dokar kulle a Bauchi
Gwamnatin jihar Bauchi ta janye dokar kulle da zaman a gida da ta sanya a wasu yankunan jihar da aka samu bullar cutar Corona.
Cikin wata sanarwa da gwamnan jihar Sanata Bala Muhammad ya fitar a larabar nan, jim kadan bayan kammala ganawa da malaman addini na jihar ta ce janye dokar kulle zai fara aiki ne daga safiyar Alhamis dinnan.
Wakilinmu Ahmad Arab Azare ya rawaito mana cewa sanarwar ta ce al’umma za su gudanar da ibadu da sauran al’amuransu amma bisa tsarin bin dokar bada tazara tsakanin juna da yawaita wanke hannaye.
Kididdigar ranar Talatar nan ta ce mutane 227 ne aka tabbatar sun kamu da cutar a jihar Bauchi, 112 daga ciki sun warke sarai an sallamesu, sai mutane 5 da suka rasa ransu sanadiyyar cutar a jiha.
Yazuwa yanzu masu dauke da cutar 107 ne ke cigaba da samun kulawar jami’an lafiya.
Karin Labarai:
Covid-19: Ku kalli yadda kasuwar tsaye ke ci yau Kaduna
Covid-19: An saka “Lock Down” a kananan hukumomi 3 na jihar Bauchi
You must be logged in to post a comment Login