Labaran Kano
Da dumi-dumi: Hisbah ta janye dokar hana cakuda maza da mata
Rahotonni daga fadar gwamnatin jihar Kano na cewa tuni gwamnati ta janye dokar nan ta hana cakuda maza da mata a baburan adai-daita sahu.
Wata majiya mai tushe daga fadar gwamnatin jihar Kano ta shaidawa Freedom Radio cewa anyi wani kwarya-kwaryar zama na musamman a yau Litinin tsakanin masu ruwa da tsaki a al’amuran addini a jihar Kano kan fara aiwatar da wannan doka, inda zaman ya cimma matsayar janye dokar har zuwa wani lokaci.
Freedom Radio ta nemi jin ta bakin babban kwamandan hukumar Hisbah ta jihar Kano, Sheikh Muhammad Haroun Ibn Sina wanda ya ce ayi masa uzri idan Allah ya kaimu gobe Talata zasu gudanar da taron manema labarai kan dokar.
Idan zaku iya tunawa dai hukumar Hisbah ta ce zata jaddada dokar hana cakuda maza da mata a baburan adai-daita sahu daga farkon shekara ta 2020 mai kamawa.
Sai dai batun ya haifar da cece kuce, musamman a kafafan sada zumunta.