Labarai
Da ɗumi-ɗumi: Kotu ta mayar da Uche Secondus kan muƙamin sa

Babbar kotun jihar Kebbi ta bada umurnin dawo da Uche Secondus a matsayin shugaban jam’iyyar PDP na ƙasa.
A Talatar da ta gabata ne wata babbar kotun jihar Rivers ta dakatar da Uche Secondus gabatar da kansa a matsayin shugaban jam’iyyar.
A zaman kotun na Alhamis din nan, mai shari’a Nusirat Umar ta bayar da umarnin a dakatar da aiwatar da umarnin baya wanda ya hana Secondus gabatar da kansa a matsayin shugaban jam’iyyar na ƙasa.
You must be logged in to post a comment Login