Labarai
Da dumi-dumi : Tsohun gwamnan jihar Kaduna ya rasu
Allah yayiwa Gwamnan tsohuwar jihar Kaduna kuma shugaban jam’iyyar PRP na kasa Alhaji Abdulkadir Balarabe Musa rasuwa da safiyar yau.
Iyalan marigayi tsohon gwamnan tsohuwar jihar Kaduna sun bayyana cewa, za a gudanar da sallar jana’izar marigayin da misalin karfe hudu na yamma.
yar marigayin Zulai Balarabe Musa ce ta bayyanawa freedom Rediyo hakan, tana mai cewa ana sa ran Dakta Gumi ne zai sallaci gawar tasa.
‘Yar marigayin wacce tsohuwar mai kula da sashen yada labarai ta hukumar kula da kafafan yada labarai na jihar Kaduna ce Hajiya Zulai Balarabe Musa.
Zulai Balarabe Musa ta bayyana cewa marigayin da ya sha fama da rashin lafiya, kafin rasuwar sa
Tana mai cewa Maihaifin nasu ya rasu ya bar Mahaifiyar su da ‘ya’ya takwas da kuma jikoki da dama.
You must be logged in to post a comment Login