Labarai
Da mutane sun san amfanin Gero a jiki da sun rikeshi a matsayin abinci-Dakta Hakeem
Masana ilimin tsirrai sun ce sinadaran Gina jiki da Gero ke dashi sun fi na sauran kayan abinci.
Masanan sun ce watsin da al’ummar yanzu su ka yi da Gero ne, yasa ake yawan samun bakin cutuka dake damun jikin dan Adam.
Shugaban cibiyar binciken Noma a kasashe masu zafi da ake Kira da Icrisat Dakta Hakeem Ajeigbe, ne ya bayyana hakan yayin taron bikin noman Gero da cibiyar ta gudanar a garin wasai dake Karamar hukumar Minjibir.
Dakta Hakeem, ya ce Gero yana da sinadarin gina jiki fiye da gabakidayan kayan abincin da al’ummar ke sarrafawa.
A cewar shi da al’umma za su rungumi amfani da Gero a matsayin abinci da ba za su rinka kamuwa da cutukan da ake samu a yanzu ba.
Da yake jawabi Hakimin karamar hukumar Minjibir Alhaji Sama’ila Abdullahi S Fulani, ya bukaci manoma da su rinka amfani da irin shuka Mai inganci da noman zamani don Samar da abinci Mai inganci ga al’umma.
Wasu daga cikin manoman da suka halarci taron sun bayyana irin alfanun da suke samu a noma.
Yayin taron an sarrafa abinci kala-kala ta hanyar amfani da gero da suka yi dai-dai a kalar abincin da al’umma ke sarrafawa a yanzu.
You must be logged in to post a comment Login