Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Da yiyuwar mu ƙarawa ma’aikatan shara alawus ɗin da ake basu – Gwamna Abba

Published

on

Gwamnatin Kano zata duba yiyiwar karawa ma’aikatan shara kudin alawus domin kyautata rayuwarsu.

Gwamna Abba Kabir Yusuf ne ya bayyana haka yayin ganawa ta musamman da ma’aikatan kwashe shara a dakin taro na Coronation dake gidan gwamnati.

Gwamna Abba wanda ya bayyana damuwarsa bisa korafe-korafen da ma’aikatan shara suka yi na tsaikon da ake samu wajen biyansu kudin alawus dinsu tsawon watanni, yace gwamnati zata yi bincike domin gano inda matsalar take da nufin maganceta cikin gaggawa.

Ya bawa ma’aikatan tabbacin gwamnati zata biyasu dukkanin basukan da suke bi tare da duba yiwuwar Kara musu kudin alawus nan bada dadewa ba.

Ya kuma yiwa ma’aikatan busharar cewa gwamnati zata tabbatar kowane ma’aikacin shara an tura shi aiki kusa da gidansa domin saukaka musu kashe kudi a wajen sufuri.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!