Labaran Kano
Dagaci ya gano maboyar batagari a Kano
Al’ummar unguwar Gandun Albasa sun koka bisa yadda batagari suka addabesu.
Dagacin yankin Gandun Albasa Injiniya Alkasim Abubakar ya bayyana rashin jin dadinsa bisa yadda batagari suka mayar da tsofaffin kamfanoni da cikin gidan Adana namun Daji gidan zoo da makabarto maboyarsu wajen aikata miyagun laifuka.
Dagacin Gandu Injiniya Alkasim Abubakar ya bayyana hakan ne lokacin taron tabbatar da tsaro a unguwannin Tukuntawa, Gandun Albasa da unguwar Sharada.
Injiniya Alkasim Abubakar ya kara da cewa mudun a’lummar yankin suka zuba ido ba tare da sun kawo karshen matsalar ba, to babu shakka abun zai girmama.
Gwamnatin Kano ta samar da na’urorin kama bata gari
Hukumar EFCC ta ce zata yi aiki da hukumar NYSC wajen dakile ayyukan bata gari
CP Wakili ya kama bata gari 200 yau a Kano
Injiniya Alkasim ya nanata cewa matukar mutane basu hada hannu wajen shawo kan matsalolin tsaro a cikin unguwannin su ba, musamman wajen jawo masu aikata laifukan a jiki toh kuwa, matsalar ka iya samun gindin zama.
Wakilin mu Abdulkarim Muhammad Abdulkarim Tukuntawa ya ruwaito mutane da dama ne suka halarci taron ciki harda baturan ‘yan sandan Sharada da sauran limaman unguwannin da masu unguwanni da al’ummar gari.
You must be logged in to post a comment Login