Kaduna
Daidan Wani: Ba titi ‘yan Kaduna ke bukata ba, a farfado da masana’antu kawai – Inji ‘yan gwan-gwan
Shugaban ‘yan gwan-gwan na jihar Kaduna Alhaji Lawal Muhammad Ya’u ya yi kira ga gwamnatin jihar da ta mayar da hankali wajen samar da masana’antu do farfado da wadanda suka durkushe.
Alhaji Lawal Ya’u ya bayyana hakan ne a zantawar sa da tashar Freedom Radio da ke Kaduna.
A cewar sa, farfado da masana’antu tare da gina sababbi zai taimaka wajen samarwa ‘yan jihar aikin yi musamman matasa.
Ya ci gaba da cewa, in har matasa suka samu aikin yi, ba sai gwamnati ta wahalar da kanta ba, wajen gyara tituna, domin al’umma da kansu za su inganta jihar.
Shugaban ‘yan gwan-gwan din yace da yawan titunan da ke fadin jihar al’umma ne suka gina a baya “Chanchangi da kanshi ya gina titunan da ke kewaye da gidan sa ba gwamnati bace ta yi”.
Shugaban ‘yan gwan-gwan din ya ja hankalin matasa da su tashi su nemi sana’ar yi don dogaro da kansu “matasa yanzu su daina tsayawa zaben sana’a duk sana’ar da suka samu su rike ta da zuciya daya”.
You must be logged in to post a comment Login