Labarai
Dakaraun Operation Haɗin Kai sun kashe ƴan ta’adda 30 a Borno

Rundunar Sojin Najeriya ta ce, Dakaraunta na Operation Haɗin Kai, sun kashe akalla ’yan ta’adda 30 a kusa da Tafkin Chadi a Jihar Borno.
Mai magana da yawun Operation Haɗin Kai, Laftanar Kanar Sani Uba, ya ce sojojin sun kuma lalata wasu kwale-kwale da ’yan ta’addan ke amfani da su wajen zirga-zirga da kai kayan aiki.
Ya bayyana cewa jiragen yakin sojoji sun dade suna sa ido a yankin, inda suka gano sama da kwale-kwale 30 na ’yan ta’adda.
A cewarsa, dakarun sun dauki mataki ne bayan samun sahihan bayanan sirri, sannan suka kai hare-hare ta sama bayan tabbatar da wuraren da maharan suke.
Hare-haren sun lalata kwale-kwalen tare da tarwatsa hanyoyin samar da kayan aikin ’yan ta’addan.
You must be logged in to post a comment Login