Labarai
Ƙungiyar Likitoci ta NMA ta dakatar da shugabanta

Kungiyar likitocin kasar nan , NMA, ta dakatar da Shugabanta na Kasa, Farfesa Bala Audu, bisa zargin karya kundin tsarin mulki da kuma aikata manyan laifuka da suka saba da dokokin kungiyar.
Dakatar da shugaban ya biyo bayan cimma matsaya a taron gaggawa tsakanin masu ruwa da tsaki na mambobin kungiyar da ya guduna Abuja wanda wakilai 63 suka halarta, ciki har da shugabanni da sakatarori daga jihohi 23 da Babban Birnin Tarayya.
An zargi Audu, wanda kuma shi ne shugaban Kwamitin Jami’an Ƙasa na ƙungiyar, NOC, da hana ‘yan takara shida shiga zaɓen ƙasa da aka tsara gudanarwa a taron shekara-shekara na NMA, a Kano daga 27 ga Afrilu zuwa 3 ga Mayu.
Taron ya kuma kafa kwamitin riƙon ƙwarya wanda tsohon Sakatare Janar Dakta Ekpe Phillips zai jagoranta domin kula da harkokin ƙungiyar kafin zaɓen.
You must be logged in to post a comment Login