Connect with us

Labarai

Dakarun Soja sun hallaka yan bindiga 9 a Katsina da Zamfara

Published

on

Dakarun soji na Operation Fansan Yamma, sun hallaka ’yan ta’adda guda tara a jihohin Katsina da Zamfara.

 

Wannan na cikin sanarwar da jami’in yaɗa labarai na rundunar, Laftanar Kanal Olaniyi Osoba ya fitar.

 

Sanarwar ta bayyana cewa an kuma kwato makamai da babura.

 

Haka kuma ya ce, a Jihar Katsina sojoji sun yi arangama da ’yan ta’adda a hanyar Turare zuwa Yantumaki da ke Karamar Hukumar Dutsinma inda suka hallaka wasu daga cikinsu.

 

Sanarwar ta kara da cewa a Jihar Zamfara an kashe wasu ’yan ta’adda ciki har da shugabanni biyu a wani samame da aka kai a Karamar Hukumar Anka, yayin da soja guda ya rasa ransa a yayin fafatawar.

 

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!