Connect with us

Labarai

Zamfara: Sojoji sun ceto mutane 5 cikin iyalan Shugaban Karamar Hukumar Bungudu

Published

on

Dakarun Rundunar Operation Fansar Yamma, sun ceto mutane 5 daga cikin iyalan Shugaban Karamar Hukumar Bungudu ta Jihar Zamfara, Nura Umar Abdullahi, bayan ’yan ta’adda sun kai hari gidansa tare da yin garkuwa da shi da wasu daga cikin iyalansa.

Hakan na ƙunshe ne ta cikin wata sanarwa da Jami’in yaɗa labaran rundunar, Laftanar Kanal Aliyu Danja, ya fitar a ranar Asabar.

Sanarwar ta ce, dakarun sun kai ɗauki bayan jin karar harbe-harbe, inda suka yi arangama da ’yan ta’addan lamarin da ya tilasta musu barin mutane 5 da suka haɗa da ’ya’yan shugaban karamar hukumar biyu, mahaifiyarsa, matarsa da wani ɗan uwansa.

Rundunar ta ce, ƴan ta’addan sun tsere zuwa cikin daji tare da shugaban karamar hukumar.

Haka kuma ta ruwaito cewa, harin ya kuma yi sanadin mutuwar ƴan sanda biyu da wani jami’in sa kai da ke cikin masu gadin shugaban, yayin da wani farar hula ya rasa ransa, sannan babban ɗan’uwan shugaban karamar hukumar, Alhaji Bello Umar, ya samu rauni.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!