Labarai
Tinubu ya nuna damuwa kan karuwar talauci a Najeriya

Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya bayyana matsalolin tsaro da talauci a matsayin manyan ƙalubale ga Najeriya, yana mai cewa suna barazana ga samar da ayyukan yi da ci gaban tattalin arziki. Ya bayyana hakan ne a bikin Ranar Ma’aikata ta duniya na 2026 da aka gudanar a Abuja, inda ya jaddada cewa ba za a samu ingantaccen aiki ba idan ma’aikata na rayuwa cikin tsoro da wahala.
Tinubu, ta bakin sakataren gwamnatin tarayya George Akume, ya ce gwamnati na daukar matakai domin magance wadannan matsaloli, ciki har da daukar matasa dubu 45 aiki a fannin tsaro da kuma fadada shirye-shiryen tallafin jama’a. Ya kuma ce an taimaka wa gidaje masu rauni miliyan 15, tare da fitar da miliyan 7.5 daga talauci.
A bangaren walwalar ma’aikata, shugaban ya bayyana cewa an fara aiwatar da sabon mafi karancin albashi, an biya bashin fansho, kuma an dawo da biyan kudin ritaya. Sai dai kungiyoyin kwadago sun bukaci karin albashi mai tsoka, inda suka nemi a kara shi zuwa Naira 225,000 musamman saboda tsadar rayuwa.
A jihohi daban-daban, gwamnoni sun yi alkawarin inganta walwalar ma’aikata ta hanyar biyan albashi a kan lokaci da daukar sabbin ma’aikata. Haka kuma wasu kungiyoyin kwadago sun nuna goyon baya ga wasu shugabanni gabanin zaben 2027, yayin da jam’iyyun siyasa ke kira ga ma’aikata su kara shiga harkokin siyasa domin inganta rayuwarsu.
You must be logged in to post a comment Login