Labarai
Dakarun Soji sun dakile harin Boko Haram da ISWAP suka kai a jihar Borno

Dakarun Soji na Operation HADIN KAI sun dakile wani harin Boko Haram da ISWAP suka kai a Gajibo da ke jihar Borno tare da cafke masu haɗa kai da ƴan taʼaddar da kuma ceto wasu mutane biyu da aka yi garkuwa da su.
Hakan na cikin sanarwar da Jami’in Yaɗa Labaran Hedikwatar Operation HADIN KAI, Laftanar Kanar Sani Uba, ya fitar a Daren jiya Talata.
Sanarwar ta ce dakarun da ke sansanin Gajibo sun gano tarin ’yan Boko Haram da ISWAP da suka taso daga wurare daban-daban a kan babura domin kai hari, amma sojojin suka tarwatsa su da manyan makamai ba tare da an rasa ko wani soja guda ba.
Haka kuma sojojin tare da haɗin gwiwar Civilian JTF sun cafke wasu mutane biyu da ake zargi da haɗa kai da Boko Haram a Gubio, sannan suka kama Umar Ahmadu a Gwoza bisa zargin kai kayan masarufi ga ’yan ta’addar.
Sanarwar ta ƙara da cewa sojojin sun ceto wasu maza biyu da aka yi garkuwa da su daga garin Mafa, yayin da wani matashi mai shekara 17 ɗan gidan wani ɗan ta’adda ya miƙa wuya bayan ya tsere daga maboyar ’yan ta’adda a tsaunukan Mandara.
You must be logged in to post a comment Login