Connect with us

Labarai

Rundunar ’Yan Sandan Jihar Katsina ta dakile hare-haren ’yan bindiga

Published

on

Rundunar ’Yan Sandan Jihar Katsina ta dakile hare-haren ’yan bindiga guda biyu a Kananan Hukumomin Kanƙara da Malumfashi tare da kubutar da mutane 12 da aka yi yunkurin garkuwa da su da kuma ƙwato dabbobi 25.

Hakan  na cikin bayanin da Kakakin Rundunar ’Yan Sandan Jihar Katsina, DSP Aliyu Abubakar Sadiq, ya wallafa.

Bayanin ya nuna cewa rundunar ta samu nasarar daƙile harin ’yan bindigar.

Haka kuma ya ce, jami’an tsaron sun samu nasarar ƙwato dabbobi 25 da maharan suka yi yunkurin tafiya da su a yayin hare-haren.

Rundunar na ci gaba da ɗaukar matakan da suka dace domin kare rayuka da dukiyoyin al’umma a faɗin Jihar Katsina.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!