Labarai
FRSC ta ƙaddamar da Operation Guduma a hanyar Abuja zuwa Kaduna

Hukumar Kiyaye Afkuwar Haɗura ta Kasa, FRSC, ta ƙaddamar da shirin Operation Guduma a kan hanyar Abuja zuwa Kaduna domin yaƙi da lodin fasinja da kaya a mota guda, lodin wuce kima da kuma amfani da lambobin mota na bogi.
An ƙaddamar da aikin ne a jiya Litinin, da aaikin ya samu kulawar wakilin shugaban FRSC na ƙasa, ACM A.M. Hassan, tare da Kwamandan Rundunar na Jihar Kaduna, yayin da Sojin ƙasar nan da Rundunar ’Yan Sanda suka samar da tsaro.
FRSC ta bayyana cewa matakin na daga cikin ƙoƙarin da take yi na tabbatar da tsaro a manyan hanyoyi da kuma ƙarfafa bin dokokin tuki da zirga-zirga.
Hukumar ta jaddada aniyarta na ci gaba da amfani da dabarun sa ido da aiwatar da doka domin rage haɗuran ababen hawa a faɗin ƙasar nan.
You must be logged in to post a comment Login