Labarai
Dalilan da suka sanya yan kasuwa kin rage farashi duk da karyewar Dala
Hawahawar farashin Dalar Amurka a fadin Nijeriya a baya ya haifar da tashin farashin kayayyakin amfanin yau da kullum wanda ya sabbaba tsadar da yan kasuwa da al’umma ke koka wa duba da yadda farashin kayayyaki ke yin tashin goron Zabi a kullu yaumin.
Sai dai duk da saukar farashin Dalar a baya-bayan nan, farashin kayayyakin na nan kamar yadda farashin canjin Dalar ya ke a baya.
Shin ko me ya janyo hakan?
Labarin bude iyakokin da gwamnatin tayyara tayi ya farantawa al’ummar kasar nan musamman ma na Arewa maso yammacin kasar, kana kuma Mako guda da fara Azumin watan ramadana ne farashin Dalar Amurka na ta sauka daga naira 1900 zuwa 1300.
Wannan tasa al’ummar Nijeriya suka fara tuhumar yan kasuwar cewa duk da koke da suka rika yi abaya na rashin tabbacin farashin Dalar Amurka, ya sanya kulluma ake samun hawhawar farashi, inda duk da saukar farashin dalar amma farashin kayayyakin bata sauya zani ba.
Alhaji Yusuf M Yusuf shugaban kungiyar Mumfarka traders dake kasuwar Kantin Kwari, cewa ya yi tabbas saukin ya samu akan kayyakin da ake sayarwa a kasuwar kantin kwari, musamman ma sababbin kaya sai dai yan kasuwar da suke da tsohon kaya ne suke sayar da kayan su a tsohon farashi.
Alhaji Yusuf kara ya bawa al’umma tabbacin samun saukin kayan da ake sayarwa a kasuwar a kantin kwari da zarar duk yan kasuwar sun kawo sababbin kaya.
Al’mma dai na fatan tabbatar da samun saukin duba da korafe-korafen da yan kasuwar suka rika yi a baya, cewa rashin tabbacin farshin kaya daga kamfanoni sakamakon tashin farashin Dalar ne ya sabbaba, inda da dama suka zubawa yan kasuwar ido don ganin yadda makomar farashin zai cigaba da kasancewa.
You must be logged in to post a comment Login