Labarai
Dalilan da suka sanya Garba Gafasa ya musanta rade-radin ya sauya sheka
Tsohon shugaban majalisar dokokin jihar Kano Abdul’aziz Garba Gafasa ya musanta rade-radin da ke yawo cewa, shi da wasu mambobin majalisar ‘ya’yan jam’iyyar APC guda goma sha hudu, za su sauya sheka zuwa jam’iyyar PDP.
Abdul’aziz Garba Gafasa ya bayyana hakan ne a wata tattaunawa da shi ta wayar tarho.
A cewar-sa, kamar yadda jama’a ke ta yada rade-radi a kafafen yada labarai game da batun, haka shima ya samu labarin da ya ce bashi da tushe ballanta makama.
A jiya litinin dai Abdul’aziz Garba Gafasa, mamba mai wakilta karamar hukumar Ajingi, ya aikawa majalisar da wasikar sauka daga mukaminsa.
You must be logged in to post a comment Login