Labaran Kano
Dalilan da suka sanya Muhuyi zai binciki zargin Ganduje da karbar Na goro
Tun a jiya ne dai hukumar karbar korafe-korafe da yaki da cin hanci da rashawa ta jihar Kano ta ce za ta binciki korafin da wata kungiya Concern for Prudent tayi kan zargin gwamnan Kano Dakta Abdullahi Umar Ganduje game da faifan bidiyon Dala.
Shugaban hukumar Muhuyi Magaji Rimingado ne ya bayyana hakan ta bakin daya daga manyan jami’an hukumar Bashir Kabir Rabi’u ya yin da yake tsokaci kan korafin da kungiya ta shigar na neman lallai hukumar ta binciki gwamnan kan zargin faifan bidiyo yana sunkume dala ajalihun sa.
Muhuyi Magaji ya ce hukumar ta karbi takardar korafi daga wata kungiya mai suna Concern for Prudent Leadership wadda ta bukaci hukumar kan ta binciki faifan bidiyon Dala da ake zargin gwamnan Kano da karbar rashawa.
Shalkwatar tsaro zata bayyana bincike badalakar tserewa da kudade naira miliyan 400
Majalisar Dattawa zata binciki ma’aikatar kula da tallafin karatu bisa zargin badakalar kudade
Muhimman abubuwan da sarkin Kano yayi a gwamnan banki
Tun da farko dai kungiyar ta Concern for Prudent Leadership ta raba takarda ga manema labarai mai dauke da sahannun Mukhtar Sani Mandawari a madadin shugaban kungiyar, inda ta nemi hukumar kan ta binciki gwamnan.
Duk da cewar gwamnan yana da shingen kariya daga tuhumar da ake masa, to amma a baya hukumar yaki da cin hanci rashawa ta kasa EFCC ta binciki tsohon gwamnan jihar Ekiti, Ayodele Fayoshe a yayin da yake karagar mulki, sannan aka dora bayan da ya sauka daga mukamin sa, a cewar kungiyar.
A dai ranar 14 ga watan Okotoban shekara ta 2018 ne aka bankado wani faifan bidiyo dake nuna ana zargin gwamna Abdullahi Umar Ganduje na sanya sinkin daloli a cikin sa.
Akan bayyanar faifan bidiyon ne ya sanya majalisar dokoki ta jihar Kano ta aikewa Shugaban jaridar Daily Nigerian Jafar Jafar da ya bayyana a gaban ta kasancewar jaridar ce ta rinka fitar da faifan bidiyon.
You must be logged in to post a comment Login