Labaran Wasanni
Dalilan da suka sanya Real-Madrid ta zama ta daya a gasar Laligar kasar Spaniya
Kungiyar kwallon kafa ta Real-Madrid ta zama ta daya a gasar Laligar kasar Spaniya, bayan ta samu nasara kan kungiyar kwallon kafa ta Real Sociedad da ci biyu da daya a daran jiya.
Yanzu dai Madrid ta yi kankankan da Barcelona wajen maki a gasar ta Laliga, inda ko wacce kungiya ke da maki 65.
A ranar juma’ar data gabata ne dai kungiyar kwallon kafa ta Barcelona tai canjaras da Sevilla ko wacce na nema 0-0, wanda hakan ne ya baiwa Madrid damar zama ta daya a gasar, bayan nasarar data samu a jiya Lahadi kan Real Sociedad.
Dalilan da suka sanya Real-Madrid ta zama ta daya a gasar ta Laliga duk da kungiyar kwallon kafa ta Barcelona ta fita yawan zura kwallaye a raga.
Yanzu dai Barcelona nada kwallaye 38, inda Real Madrid ke da kwallaye 36.
Kamar yadda yake a tsarin gasar ta Laliga idan kungiyoyi suka yi canjaras ana fara duba kungiyar dataci wata a gasar sai ta zama ta daya.
A bana wasan farko tsakanin Real-Madrid da Barcelona daya gudana a ranar Lahadi 27 ga watan Octoban wasan daya gudana a filin wasa na Santiago Bernebau inda aka tashi kowacce kungiya na nema.
Sai kuma wasa na biyu daya gudana a ranar 1 ga watan Maris din daya gabata a filin wasa na Comp Nou, wanda Real Madrid ta samu nasara kan Bacerlona da ci 2-0
Nasarar da Madrid ta samu kan Barcelonan a ranar ta 1 ga watan na Maris shine ya bata damar zama ta daya a gasar ta Laliga.
Zuwa yanzu dai an buga wasanni 30 a gasar ta Laliga, inda ya rage wasanni 8 a karkare gasar ta bana.
You must be logged in to post a comment Login