Labarai
Dalilan ECOWAS ta janye tankunkuman da ta sanya wa wasu kasashe
A wani yunkuri na tabbatar da zaman lafiya da bunkasa tattalin arzikin kasashen yammacin Afirka, kungiyar ECOWAS ta yanke shawarar janye takunkumin tattalin arziki da ta kakabawa jamhuriyar Nijar, da Mali da kuma Guinea-Bissau.
An cimma wannan matsaya ne a yayin wani taro na musamman da ya shafi zaman lafiya, siyasa, da tsaro na kasashen ECOWAS, wanda aka gudanar a jiya Asabar a birnin tarayya Abuja.
ECOWAS ta yanke shawarar dage wasu takunkumin tattalin arziki da ta kakabawa Guinea, Bugu da kari, an kuma sassauta takunkumin da aka kakabawa kasar Mali a wani bangare na kudurin kawo zaman lafiya a kasar.
You must be logged in to post a comment Login