Labarai
Dalilin da ya sanya ake ci gaba da tsare Ibrahim Magu
Bayan da aka yi zargin cewa mukaddashin hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta EFCC Ibrahim Magu na da lam’a a jikin sa, har kawo ranar Alhamis tswon kwanaki 4 kenan yana tsare.
Ana zargin cewa Magun ya aikata wasu manyan laifuka da suka hadar da sace kudaden da aka sato da sayar da kadarorin da aka kwato da kuma mayar da wasu jami’an hukumar ta EFCC shafaffu da mai wajen gudanar da ayyukan bincike da dai sauran su.
Kawo yanzu mukaddashin hukumar EFCC na fuskantar kwamitin bincike da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kafa kan zarge-zargen da ake masa.
Karin labarai:
Kwamitin fadar shugaban kasa ya gayyaci wasu manyan jami’an hukumar EFCC
Hukumar EFCC ta gano ma’aikatan bogi 1000 a jihar Kwara
Kwamitin wanda tsohon babban alkalin kotun daukaka kara mai shari’a Ayo Salami ke jagoranta ya yin da kuma akwai hukumomin tsaro da suka hada da ‘yan sanda da jami’an DSS a matsayin wakilan kwamitin.
Ministan shari’a kuma Atoni janaral ne ke zargin Magun da aikata wadancan laifuka.
Rahotanni sun bayyana cewar, tun a shekarar 2015 ne ake samun sabani tsakanin Magu da Abubakar Malami.
‘Yan Najeriya na zuba ido don ganin yadda zata kaya da zarge-zargen da ake yi wa Magun idan har sun tabbatar da su bayan da aka dakatar da shi daga kan mukamin sa.
You must be logged in to post a comment Login