Connect with us

Labarai

Kwamitin fadar shugaban kasa ya gayyaci wasu manyan jami’an hukumar EFCC

Published

on

Kwamitin fadar shugaban kasa da ke binciken zarge-zargen cin hanci da rashawa da ake yiwa dakataccen shugaban hukumar EFCC, Ibrahim Magu, ya gayyaci sakataren hukumar ta EFCC, Olanipekun Olukoyede, da wasu daraktocin hukumar a ranar Alhamis.

Majiyar PUNC ta tattaro wasu bayanai da ke cewa an gabatarwa da jami’an hukumar tambayoyi a kan zargin karkatar da wasu kudade da aka kwato daga hannun barayin gwamnati.

An samu labarin cewa an gayyato manyan jami’an hukumar ta EFCC ne kan ko dai su kawo hujjoji ko kuma su bayar da wasu bayanai da Magun yayi a gaban kwamitin.

Baya ga zargin karkatar da kudaden da aka kwato, ana kuma zargin Ibrahim Magu da siyarwa ko sakin wasu tankokin mai guda 157 da aka kwace a Fatakwal ba tare da bin tsari ba.

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Freedom Radio Dutse 99.5 FM Dala FM Kano 88.5

Now Streaming

Archives

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.

error: Content is protected !!