Connect with us

Siyasa

Dalilin da ya sanya Gwamna Abba ya ajiye jar hula a Faransa

Published

on

Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya jawo cece-kuce bayan ya bayyana ba tare da jar hularsa ba a wani taro a birnin Paris na ƙasar France.

 

An gan shi a wajen baje kolin noma na ƙasa da ƙasa, wato Paris International Agricultural Show, inda yake halartar taruka domin ƙarfafa haɗin gwiwar noma da jawo hannun jari zuwa Kano.

 

Bayyanarsa ba tare da jar hula ba ta haddasa muhawara a kafafen sada zumunta, musamman ganin cewa hular na da alaƙa da tafiyar Kwankwasiyya da kuma tsohon jagoransa, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso.

 

Sai dai da aka tuntubi mai magana da yawun gwamnan, Mustapha Muhammad, ya ce babu wata manufa ta siyasa a cikin lamarin, yana mai cewa salon suturar “casual” ne kawai, kuma gwamnan kan cire jajayen hular idan yana ƙasashen waje.

 

Ya kuma jaddada cewa yanayin taruka da ƙa’idojin ƙasashen waje kan shafi yadda ake sanya kaya, don haka bai kamata a ɗora masa wata ma’ana ta siyasa ba.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!