Labarai
Dalilin da ya sanya jami’an KAROTA basu fito aiki ba – Baffa
Hukumar KAROTA ta ce dalilin da ya sa ta hana jami’anta fita aiki ranar Lahadi shine, sun samu rahoton cewa akwai wasu ‘yan bindiga da ke kokarin kai musu farmaki.
A cewar hukumar hakan ta sanya rundunar ‘yan sanda tura jami’anta aikin sintiri a fadin Kano, domin shirin ko ta kwana, bayan da ta shawarci KAROTA da ta janye jami’anta.
Shugaban hukumar KAROTA Baffa Babba Dan-Agundi wanda ya bayyana hakan a wani sakon jawabi da ya fitar, ya tabbatar da cewa an samu rikici tsakanin wani jami’insu da wani mutum da ya karyawa kafa, kuma yanzu haka yana hannun jami’an ‘yan sanda.
Hukumar KAROTA ta musanta rade-radin da ake yadawa a kafafen sada zumunta cewa an samu rashin fahimtar juna tsakanin ta da rundunar ‘yan sanda ta jihar Kano.
Hukumar ta KAROTA ta ja hankalin jama’a da su daina yada labaran karya a kafafen sada zumunta, la’akarin da irin illar da hakan ke da shi.
You must be logged in to post a comment Login