Labarai
Dambarwar siyasa ta kaure tsakanin hadiman Ganduje a Facebook
Dambarwar ta ɓarke bayan wani saƙon murya da ya karaɗe kafafen sada zumunta.
A cikin saƙon an jiyo Gwamna Abdullahi Umar Ganduje na yin kakkausan kalamai ga ƙungiyar Kwankwasiyya ta tsohon Gwamna Kwankwaso.
Ga Muryar Gwamna Ganduje.
Yayin da mutane ke ta bayyana ra’ayoyinsu kan wannan batu, sai hadiman Gwamna Ganduje suka bi sahu.
Tsohon kwamishinan ayyuka a Gwamnatin Ganduje Engr. Mu’azu Magaji ya wallafa a shafinsa na Facebook cewa.
“Wannan maganar da mai girma Gwamna ya yi a baya, ai ba ta yau ba ce, ya yi tane lokaci da ake kan zafin rarrabuwa”.
Ya ci gaba da cewa, “A yau Gwamna Ganduje uba ne kuma shugaba ga dukkan mutanen Kano har da su ƴan Kwankwasiyyar”.
“Don haka a matsayinsa na uba kuma dattijo, ba zai yi irin wannan kanbun bakin kan al’ummarsa ba, komai banbancin ra’ayin siyasa.
Ku kalli cikakken bayanin da Engr. Mu’azu Magaji ya wallafa.
Wannan Maganar da Maigirma Gwabna ya yi a baya ai ba ta yau bace, yayi tane lokacin da ake kan zafin rarrabuwa….
Ayau…
Posted by Muaz Magaji on Tuesday, 19 January 2021
Da alama wannan batu na Ɗan Sarauniya bai yiwa wasu cikin hadiman Ganduje daɗi ba.
Ba jimawa sai Mai taimakawa Gwamnan kan kafafen sada zumunta Abubakar Aminu Ibrahim ya yi martani a nasa shafin.
A cewar Abubakar, “Oga Win Win (Mu’azu Magaji) wannan magana da Oga (Gwamna Ganduje) ya yi ta ne ranar Jumu’a, ana gobe zaɓen ƙananan hukumomi”.
Ya ci gaba da cewa, “Idan ma kwangila Kwankwaso ya baka na shirya su da Baba Ganduje to ka je ka mayar, domin sai mun binne shi a siyasa za a yi sulhu”.
Oga Win Win wannan Magana fa Oga yayita ne ranar Juma’a ana gobe Zaben Kananan Hukumomi.
Inma kwangila Kwankwaso…Posted by Abubakar Aminu Ibrahim on Tuesday, 19 January 2021
Yanzu haka dai tuni wannan batu ya ke ta ci gaba da ɗaukar hankulan jama’a, inda da dama ke bayyana ra’ayoyinsu a kai.
You must be logged in to post a comment Login