Labarai
Dan majalisar wakilai daga jihar Filato ya rasu
Dan majalisar wakilai mai wakiltar mazabar Jos ta arewa da Bassa Alhaji Haruna Maitala ya rasu sakamakon wani hatsarin mota da ya ritsa da shi a jiya juma’a.
Rahotanni sun ce hatsarin motar ya ritsa da dan majalisar ne akan hanyar Abuja zuwa Jos.
Ya kuma mutu ne a cibiyar lafiya ta gwamnatin tarayya da ke garin Keffi a jihar Nassarwa, sakamakon raunin da ya samu.
Mai magana da yawun dan majalisar, Joseph Audu, ta cikin wata sanarwa da ya fitar, ya shaidawa manema labarai cewa, da safiyar yau Asabar ake sa ran gudanar da jana’izar sa kamar yadda addinin musulunci ya koyar.
You must be logged in to post a comment Login