Kiwon Lafiya
Dan takarar jam’iyyar PDP ke kan gaba yayin da aka samu hargitsi a karamar hukumar Nasarawa
Dan takarar jam’iyyar PDP Abba Kabiru Yusuf shi ne a kan gaba yayin da ake cigaba da ‘yaryaga takardun sakamakon zaben gwamnan da ake yi a jiya da daddare.
Yayin da gwamnan jihar Kano Abdullahi Umar Ganduje yake biya masa, sai kuma jam’iyyar PRP take mara mata baya.
Baturin zabe na jihar Kano Farfesa B.B Shehu na jami’ar jihar Kebbi na cigaba da tattara sakamakon zaben kafin a kawo harin tada hargitisi.
Haka zalika rahotanni sun bayyana cewar, sakamakon zaben na nuna cewar jam’iyyar PDP inda take da kuri’u fiye da dubu 951 da dari 531 yayin da kuma jam’iyyar APC ke da kuri’u dubu dari 935,451.
Wanda hakan ke nuna cewar, jam’iyyar PDP ce ke kan gaba.
Yayin da offishin zabe dake nan Kano ya dage zaman tattara sakamakon kawo yanzu.