Connect with us

Kiwon Lafiya

Rundunar yan sandar jihar Kano ta kama mataimakin gwamnan Kano

Published

on

Rundunar ‘yan sanda ta jihar Kano ta kama Mataimakin gwamnan jihar Kano Nasiru Yusuf Gawuna da kwamishinan kananan hukumomi Murtala Sule Garo da shugaban karamar hukumar Nasarawa Lamin Sani saboda zargin kawo hargitsi a yayin da ake kokarin tattara sakamakon zabe.

Rahotanni sun bayyana cewa, ana zargin su da kai hari ofishin tattara sakamakon zabe da misalin karfe 1 da minti 30 tare da ‘yan bangar siyasa  wanda suka sanya tsoro a zukatan mutane kafin jami’an tsaro su kawo dauki.

Jaridar Solacebase ta rawaito cewa kawo yanzu ana dakwan karamar hukumar Nassarawa kawo yanzu bayan da aka sanar da sakamakon zaben kananan hukumomi 43.

Jami’an ‘yan sandan dai sun dauke wanda ake zargin zuwa shalkwatar rundunar dake Bompai ana Kano.

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Freedom Radio Dutse 99.5 FM Dala FM Kano 88.5

Now Streaming

Subscribe to Freedom Radio via Email

Enter your email address to subscribe to this site and receive notifications of new posts by email.

Join 338,762 other subscribers.

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.

error: Content is protected !!