Labarai
Dan takarar shugaban kasa karkashin jami’yyar PDP ya gaza sa hannun yarjejeniyar zaman lafiya
Fadar shugaban kasa ta yi kira ga kwamitin samar da zaman lafiya na kasa da ta dauki mataki kan jam’iyyar PDP tare da dan takarar shugaban kasar ta, sakamakon gaza sanya hannu kan yarjejeniyar zaman lafiya da aka gudanar a watan da ya gabata.
A wata sanarwa mai dauke da sa hannun babban mai taikamawa shugaban kasa kan harkokin yada labarai Malam Garba Shehu ya kalubalanci jam’iyyar PDP da cewa basa nufin kasar nan da alkahiri musamman zaman lafiya a yayin zaben badi.
Ya kuma kara da cewa ko da kalubalantar iyalan shugaban kasa da wata kungiya da ke goyon bayan Atiku ke yi ya karya ka’idojin da kwamitin samar da zaman lafiya ya tanadar ne.
Ya kuma kara da cewa kungiyar ta kalubalanci iyalan shugaban kasa da cin hanci da rasahawa da yin abin da bai kamata ba, amma har Yanzu jam’iyyar PDP bata tsawatar dangane da hakan ba, abinda ke cewa tana da wata boyayyiyar manufa kan tayar da tarzoma, kuma maimakon ta tsawatarwa kungiyar sai ma kara ta’azzara al’amarin da suke yi.
Sannan yace babban abin kunya ne jam’iyyar PDP ta rika yada wadannan kalamai ba tare da kwakwarar hujja ba.