Connect with us

Labaran Wasanni

Dan wasan Kano Pillars ya bata – Malikawa Garu

Published

on

 Kungiyar kwallon kafa ta Kano Pillars ta sanar da batan daya daga cikin ‘yan wasanta mai suna Sunday Chinedu.

Jami’in hulda da jama’a na kungiyar Lurwan Idris Malikawa Garu ne ya sanar da hakan yayin zantawa da freedom Raadio.

A cewarsa tun farko mai hora da ‘yan wasan Pillars Lionel Soccio ya bashi hutun kwanaki hudu da ya ziyarci iyalansa amma sai gashi yanzu sati biyu ke nan ba aji duriyarsa ba.

Rilwan Idris Malikawa ta cikin sanarwar ya kuma ce, Sunday Chinedu bai sanar da kungiyar halin da yake ciki ba saboda haka ne yasa kungiyar ta sanar da batansa.

Marseille ta bude makarantar wasanni a Najeriya

COVID-19: ‘Yan wasan Newcastle sun dawo sansanin daukar horo

A bangare guda shugaban kungiyar ta Kano Pillars Shu’aibu Surajo ya bai wa dan wasan wa’adin kwanaki uku da ya dawo ko kuma a dauki matakin ladaftarwa a kansa.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Freedom Radio Dutse 99.5 FM Dala FM Kano 88.5

Now Streaming

Subscribe to Freedom Radio via Email

Enter your email address to subscribe to this site and receive notifications of new posts by email.

Join 338,433 other subscribers.

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.

error: Content is protected !!