Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labaran Wasanni

COVID-19: ‘Yan wasan Newcastle sun dawo sansanin daukar horo

Published

on

Kungiyar kwallon kafa ta Newcastle United ta bude filin horas da ‘yan wasanta da aka rufe sakamakon karuwar annobar cutar Corono.

An dai rufe filin wasan ne a ranar Litinin makon jiya bayan samun karuwar masu dauke da cutar cikin ‘yan wasan da aka yiwa gwaji.

Kungiyar ta kuma ce an killace ‘yan wasan da suka kamu da COVID-19 din tare da cigaba da karbar magani kafin su dawo filin daukar horon.

A sakamakon hakan ne kungiyar ta gaza samun damar horas da ‘yan wasan nata baki daya yayin da suke shirin karawa da Aston Villa a wasanta na farko a gasar Premier League, lamarin da ya sanya aka dake wasan a makon jiya.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!