Labaran Wasanni
Dan wasan Najeriya ya kamu da Corona
Dan wasan gaba na kungiyar kwallon kafa ta kasa Super Eagles, Paul Onuachu dake wasa a kungiyar kwallon kafa ta Genk dake kasar Belgium ya kamu da cutar Corona a gwajin da a ka gudanar ga ‘yan wasan dake buga wasa a kasar.
Sai dai sakamakon da a ka samu na ‘yan wasan kasar nan da suma suke wasa a kungiyar Heracles Almelo dake kasar ta Belgium wato Stephen Odey da Cyril Dessers ya nuna cewar basa dauke da cutar.
Paul Onuachu mai shekaru 26 shi ne dan wasan farko na kungiyar kwallonn kafa ta kasa Super Eagles da a ka samu dauke da cutar ta Corona cikin ‘yan wasan kungiyar dake wasa a kasashen ketare da a ka yi mu su gwajin cutar a kungiyoyin su.
Onuachu yabar kasar nan zuwa kasar ta Belgium a ranar 27 ga watan Mayun da ya gabata, domin halartar kungiyar sa a kasar ta Belgium.
Onuachu dai shi ne dan wasa na biyu a kasar nan da ya kamu da cutar, tun bayan da Akpan Udoh, ya kamu da cutar a watan Fabrairun da ya gabata.
You must be logged in to post a comment Login