Labarai
Dangote na shirin gina matatar mai ta Dala biliyan 17 a Kenya

Kamfanin manfetur na Dangote ya sanar da cewa yana shirin gina babbar matatar mai ta kimanin dala biliyan 17 a ƙasar Kenya, aikin da ake sa ran zai ƙarfafa fannin makamashi a Gabashin Afirka tare da rage dogaro da shigo da tataccen mai daga ƙasashen waje.
A cewar kamfanin, an kammala zaɓen wurin da za a gina matatar, ana ci gaba da gwajin ƙasa, yayin da aka fara ayyukan zane da taswirar aikin.
Ana sa ran matatar za ta fi samar da man fetur ga Kenya da maƙwabtan ƙasarta.
Kamfanin na Dangote ya ce za a gina matatar a yankin Lamu da ke gabar tekun Kenya, kuma ana sa ran za ta kasance mai kama da babbar matatar Dangote da ke Nijeriya.
You must be logged in to post a comment Login