Labarai
Masarautar Kano ta amince da yin murabus din dagacin Rugu-rugu

Mai martaba Sarkin Kano Khalifa Muhammadu Sanusi na biyu ya amince da yin murabus din Dagacin garin rugu-rugu da ke karamar hukumar tudun Wada Malam Bello Muhammad mai shekaru tamanin da biyar a duniya sakamakon rashin lafiya da yake fama da ita.
Dagacin ya shaida wa sarkin cewa shi ne da kansa ya ke son yin murabus ba wanda ya sa shi saboda yanzu tsufa ya kama shi ba zai iya aikin ba.
Mai martaba Sarkin ta bakin babban dan majalisar sarki Matawallen Kano Alhaji Aliyu Ibrahim yace an amince da yin murabus dinsa da sharadin ba zai kawo wanda za’a nada sabon dagacin ba sai wanda mai martaba sarki ya amince da shi.
inda ya ce, ya yarda da hakan, kuma masarautar Kano ta bada damar a shirya yi masa murabus.
A nasa jawabin Malam Sani Bello da ga dagacin mai murabus ya gode wa masarautar Kano a madadin zuri’ar gidansu bisa amincewarta da yin murabus din mahaifin nasu.
You must be logged in to post a comment Login