Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Dino Melaye ya gabatar da kudiri kan masu garkuwa da mutane

Published

on

Majalisar dattijai ta bukaci hukumomin tsaron Najeriya  da su karfafa harkokin tsaro domin kare rayukan al’umma da kuma dukiyoyinsu, mussamman wadanda suke yawan tafiye-tafiye a hanyar Abuja zuwa Lokoja da wasu titunan da ke kasar nan.

 

Wannan matsaya dai ta biyo bayan wani kudiri da Sanata Dino Melaye na jami’yyar PDP da ke wakilta Kogi ta yamma ya gabatar duba da yawaitar kame mutane tare da yin garkuwa da su a mafi yawan lokuta ma har ta kai ga sun rasa rayukansu.

 

Sanata Dino dai ya gabatar da wannan kudiri ne karkashin doka ta 42 da ta 52 na dokar majalisar,inda ya ce mutane 8 da aka yi garkuwa da su a ranar 11 ga watan Satumban da ya gabata , yayin da aka sake yin garkuwa da wasu mutane 11 a ranar 18 ga satumban da ta gabata.

 

Har ila yau dai a dai a ranar 24 ga dai satumba ne kuma aka sake garkuwa da wasu mutane 18, mutane 8 daga cikinsu sun hadar da manyan jami’an gwamnati ciki harda dan sanda wanda ya rasa ransa.

 

Ya ce kawo yanzu babu wani yunkurin da aka yi na kare dukiyoyin al’umma, wanda ya ce kare rayuka da dukokiyin alumma na daga cikin hakkokin majalisar.

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!