Labarai
Dokar kulawa da lafiyar mata da kana nan yara zata rage mutuwar mata masu juna biyu- CHRICED
Cibiyar kare hakkin Dan-adam da wayar da kan yan kasa wato Resource Center For Human Rights and Civic Education, ta ce, sahale dokar kulawar lafiya ga mata masu juna biyu da kananan yara kyauta da majalisar dokokin Kano ta yi, a matsayin hanyar rage mutuwar mata da jarirai a fadin kasar nan’.
Shugaban cibiyar Dr Ibrahim Zikirillah ne ya bayyana hakan a ganawarsa da manema labarai da yammacin jiya a nan Kano.
Dr Ibrahim Zikirillah, wanda jami’ar gudanar da ayyuka ta cibiyar Zuwaira Umar Muhammad, ta yi jawabi da Hausa a madadinsa, ta ce, ‘za a samu saukin raguwar mace-mace mata da jarirai har ma da kananan yara a fadin kasar, matukar gwamna Ganduje ya sanya hannu kan doka kuma ta fara aiki’.
Jami’ar ta kuma yaba wa majalisar dokoki da majalisar masarautar jihar Kano bisa rawar da suka taka wajen ganin an samu nasarar yin dokar.
majalisar dokokin jihar Kano ta sahale dokar ne a zamanta na jiya Laraba bayan da ta kammala aikin taza da tsifa a kanta.
Rahoton: Auwal Hassan Fagge
You must be logged in to post a comment Login