Kasuwanci
Dokar masana’antar man fetur ba ta da alaƙa da ƙarin farashin mai – PPPRA
Hukumar ƙayyade farashin albarkatun man fetur ta ƙasa PPPRA ta ce, sanya hannu kan dokar masana’antar man fetur baya nufin ƙarin farashin litar mai a ƙasar nan.
Shugaban hukumar Abdulkadir Sa’idu ne ya bayyana hakan a Abuja.
A cewar sa, abin a taya shugaban ƙasa Muhammadu Buhari da ministan albarkatun man fetur Timipre Sylva murna ne, kan yadda suka yi ƙoƙari wajen tabbatar da dokar mai dumbin tarihi.
Karin farashin wuta da man fetur ya nuna Najeriya na cikin halin ni’yasu – Masani
Abdulƙadir Sa’idu ya kuma ce, dokar za ta bada dama wajen bin dokokin shugabanci da kuma ƙa’idoji a masana’antar man fetur, baya ga ciyar da ita gaba.
You must be logged in to post a comment Login