Labarai
Don biyan bukatar aljihu kawai ake film a yanzu –Bosho
Don biyan bukatar aljihu kawai ake film a yanzu –Bosho
A wata tattaunawa da fitaccen jarumin barkwancinnan Sulaiman Hamma wanda akafi sani da Bosho yayi da Freedom Radio ya bayyana cewa “banbancin dake tsakanin fina-finan da, dana yanzu shine a da ana yin film ne don kishi da cigaban yarenmu na Hausa, amman yanzu ana yin film dinne domin cigaban aljihu kawai”
Sulaiman Bosho ya kara da cewa babban kalubalen da yake fuskanta a harkarsa ta film shine rashin samun kyakykyawar fahimta daga mutane, domin kuwa a mafi yawan lokuta idan ya hadu da jama’a sai yaga suna tsammanin suga yayi musu abinda suke ganin yanayi a film sabanin cewa komai akwai muhallinsa.
A bangaren nasarori kuwa Sulaiman Bosho ya bayyana cewa “Alhamudlillahi naje inda ban taba zuwa ba, na mallaki abinda ban taba tsammanin zan mallaka ba”.
A karshe ya bayyana babban burinsu shine ganin masana’antar Kannywood tayi kafada da kafada da sauran manyan masana’antun fina-finai na duniya.
Ko yaya kuke kallon wannan batu?