Labaran Kano
Dr Habib Lawal:Sanya hannun yarjejeniyar cire shingen kasuwanci Afrika zai bunkasa tattalin arzikin
Wani masanin tattalin arziki a nan jihar Kano, ya ce, sanya hannu kan yarjejeniyar gudanar da kasuwanci ba tare da shinge ba tsakanin kasashen Africa, lamari ne da zai taimaka gaya wajen bunkasa tattalin arziki musamman wajen inganta bangaren wutar lantarki.
Dr. Habib Lawal Yahya wanda kuma malami ne a kwalejin Fasaha na Jihar Kano, ya bayyana hakan ne ta cikin shirin Labaran ‘Muleka Mugano’ na Freedom Rediyo wanda ya mai da hankali kan batun yarjejeniyar da shugabanni afurka suka sanya hannu a kai a baya-bayan nan.
Ya kuma ce, kamata yayi kasashen Afurka su yi la’akari da yadda sauran kasashen Turawa su ka ci gajiyar gudanar da kasuwanci ba tare da shinge ba, wanda ya taka rawa wajen bunkasa tattalin arzikin nahiyar.
Dr. Habib Yahya ya kuma nanata cewa, matukar aka fara gudanar da shirin na kasuwanci ba tare da shinge ba, lamura za su kyautatu a nahiyar Afurka.
A cewar sa, wannan yarjejeniyar za ta zaburar da sauran kasashen da ke nahiyar wajen bunkasa tattalin arzikin su.