Kiwon Lafiya
Zabe:Akwai bukatar sake wayar da Kan ma’aikatan wucin gadi na hukumar INEC
Masanin kimiyyar siyasar a jami’ar Bayero ta Kano Dr Saidu Ahmad Dukawa ya bayyana cewa akwai bukatar sake wayar da kan ma’aikatan wucin gadi na hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa INEC gabanin gudanar da zaben gwamnoni da na ‘yan majalisar jihohin wanda za’a yi a ranar Asabar 9 ga wannan watan na Maris.
Dr Saidu Ahmad Dukawa ya bayyana hakan ta cikin shirin ‘Mu leka Mu Gano’ na musamman na nan tashar Freedom Radio wanda ya mayar da hankali kan yadda aka gudanar da zaben a ranar 23 ga watan jiya na Fabarairun.
Masanin ya ce akwai Kurakurai da aka tafka a wasu daga cikin cibiyoyin zabe sakamakon rashin gudanar da aiki yadda ya kamata da na’urorin tantance katin zabe Card Reader yayin tantance masu kada kuri’a.
Da yake bayani kan wuraren da aka yi zargin cewa wakilan wasu jami’yyu na dangwala wa wadanda suka zo zabe ba tare da sanin kowace jam’iyya za su zaba ba, Masanin kimiyyar siyasar ya ce bisa dokar hukumar zabe mai zaman kan ta kasa INEC soke irin wadannan kuri’u ake yi.
Dr Sa’idu Ahmad Dukawa ya kuma bayyana cewa rashin fitowar mutane sosai a rumfunan zabe da aka saba gani a sauran zabukan da suka wuce, hakan ba zai rasa nasaba da halin kunci da ‘Yan Najeriya ke ciki da kuma tunanin da wasu ke yi na rashin adalci a tsakanin shugabanni da yawanci suke wa wadanda suke jagoranta, kasancewar hakan ya dar su a zukatan su.