Connect with us

Labarai

Jami’an DSS sun kama masu hannu a garkuwa da daliban jihar Neja

Published

on

Hukumar tsaron farin kaya ta Najeriya DSS ta kama mutum biyar ciki har da suka haɗa da ’yan ƙasar Nijar biyu, waɗanda ake zargi da safarar makamai ga ’yan bindigar da suka kai hari makarantar Katolika ta St Mary’s da ke ƙauyen Papiri a jihar Neja a ranar 21 ga Nuwamban 2025, inda suka sace ɗalibai da ma’aikata akalla 300.

 

An ƙwato tarin makamai daga hannun mutanen, ciki har da bindigogin AK guda 15 da harsasai masu rai guda 1,434, kamar yadda gidan talabijin na Channels ya ruwaito.

 

A cewar wasu majiyoyin tsaro, an kama Yusuf Mohammed da ake kira Bature, wanda ke cikin jerin waɗanda ake nema na ƙungiyar Jama’atu Ahlis Sunna Lidda’awati wal-Jihad (Boko Haram), tare da abokin aikinsa Mubarak Ibrahim a kan hanyar Zaria zuwa Kaduna yayin da suke kan hanyarsu ta karɓar wasu makamai domin kai wa shugabanninsu.

 

Majiyar ta ƙara da cewa wani samame da aka biyo baya ya kai ga kama Goni Ibrahim, wani mai safarar makamai na ƙasa da ƙasa daga yankin Diffa na Jamhuriyar Nijar. An kuma kama Tukur Sani tare da shi, wanda aka bayyana a matsayin abokin aikinsa.

 

Majiyoyin tsaron sun ce an kama mutanen biyu ne a cikin wata mota mai launin shuɗi da ba a bayyana sunanta ba, tare da bindigogin AK-103 guda 15, mujallun harsasai guda 15, da harsasai na 7.62mm guda 1,434.

 

Bayan kwanaki kaɗan da kama waɗannan mutane, jami’an tsaro sun sake kama wani da ake zargi yana cikin ƙungiyar masu safarar makaman mai suna Alhaji Adamu wanda aka fi sani da Gado Banufe, a garin Yauri da ke jihar Kebbi. Ana zarginsa da samar da makamai a yankin Kebbi.

 

Majiyoyin tsaron sun bayyana cewa binciken farko ya nuna cewa mutanen biyar na daga cikin masu safarar makamai ga ’yan bindigar da suka kai harin makarantar kwana ta Katolika da ke Papiri a watan Nuwamban 2025.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!