Labarai
Dole a ceto dalibai da malamai da aka sace a Oyo – Kwankwaso

Tsohon gwamnan Kano Rabiu Musa Kwankwaso ya bayyana damuwarsa matuƙa kan halin da dalibai da malamai da aka sace daga makarantu a karamar hukumar Oriire da ke jihar Oyo ke ciki.
Ya bukaci gwamnatin Nijeriya da ta dauki batun ceton su a matsayin abin gaggawa, tare da ɗaukar tsauraran matakan da za su hana irin waɗannan hare-hare da sace-sace sake faruwa a nan gaba.
A cewarsa, wajibi ne Nijeriya ta kuɓuta daga matsalar rashin tsaro da ke addabar ƙasar, yana mai jaddada cewa kare rayuka da mutuncin kowane ɗan ƙasa ya zama babban nauyi ga gwamnati.
You must be logged in to post a comment Login